Kusan kowanne farkon shekarar bature, al’umma da dama suna kallon lokacin a matsayin lokacin hutu da shakatawa kama daga masu kudi, sanannanun mutane da masu mulki musamman a kasashen turawa da wajen ‘yan Bokon mutan yammacin Afirika.
DABO FM ta duba yacce sanannun mata a masa’antar fina-finan Hausa ta Kannywood suke irin tasu hutawar, kama daga zuwa Umara har zuwa sauran manyan biranen hutu na duniya.
Zamuyi duba akan jarumai irinsu Fati Washa, Hadiza Gabon, Rahama Sadau, Maryam Ceeter da Aishatul Humaira.
Rahama Sadau
Yanzu haka, fitacciyar jarumar tana hutunta a kasar birnin Paris na kasar Faransa wanda alamu sun nuna bata har yanzu bata shafe sama da kwanaki 2 a garin ba.
Maryam Ceeter
DABO FM ta tabbatar da cewa zuwa yanzu da muke hada wannan rahotan, jaruma Maryam Ceeter tana kan hanyar dawowarta daga hadaddiyar daular larabawa. Kafin ta kaje birnin Dubai, ta fara zarzayawa kasar Saudiyya domin sauke yin Umara.
View this post on Instagram
Fati Washa da Hadiza Gabon
Jaruman guda biyu a yanzu haka suna birnin Dubai tare da wasu abokan sana’arsu da suka hada da Nasiru Aliko.
Aishatul Humaira
Ita ma dai jaruma Aisha Humaira tana chan a birnin Dubai domin hutawa. Kafin tafiyarta birnin Dubai, taje kasar Saudiyya domin Umara.
