Home LabaraiBuhari zai bar Najeriya zuwa Landan kafin yanke hukuncin zaben Kano, Bauchi da Sokoto

Buhari zai bar Najeriya zuwa Landan kafin yanke hukuncin zaben Kano, Bauchi da Sokoto

by Dabo Online
0 comments
Buhari Travels

A ranar Juma’a, shugaba Muhammadu Buhari zai bar Najeriya zuwa birnin Landan domin halartar taron zuba hannayen jari tsakanin Burtaniya da kasashen Afirika a ranar 20 ga watan Janairu.

Mai magana da yawun shugaba Buhari, Femi Adesina, ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Alhamis.

Firaministan Burtaniya, Boris Johnson ne ya shirya taron, wanda a cewarsu zai kara hada kawunan shuwagabannin Afirika tare da bunkasa kasuwancin su wanda zai samar da karuwar alaka a tsakani da samar da ayyukanyi tsakanin al’umnar nahiyar Afirika da kasar Burtaniya.

Femi Adesina, ya bayyana cewar shugaba Muhammadu Buhari zai dawo Najeriya a ranar Alhamis ta sati mai zuwa.

A ranar Juma’a ne dai ake sa ran kawo karshen shari’ar gwamnan jihar Sokoto da jami’iyyar APC take kalubalantar nasarar gwamna Aminu Waziri Tambuwal.

Inda a daya bangaren kuma, ranar 20 ga watan Janairun 2020, kotu koli ta ayyana ranar a matsayin ranar da zata yanke hukuncin shari’ar gwamnan Kano da jami’iyyar PDP da dan takararta, Engr Abba Kabir Yusuf suke kalubalantar nasarar gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00