Home LabaraiJami’an SARS sun kashe mayakan Boko Haram da dama a wata arangama da sukayi a Borno

Jami’an SARS sun kashe mayakan Boko Haram da dama a wata arangama da sukayi a Borno

by Dabo Online
0 comments

Jami’an SARS a jihar Borno sun fatattakin mayakan Boko Haram da sukayi kwanton bauna a kauyen Mainok dake kan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri.

Rahotanni sun bayyana yadda mayakan Boko Haram suka fara harbin jami’an SARs wanda daga bisani jami’an na SARS suka fatattake su.

Majiyoyi sun bayyanawa PRNigeria cewar jami’an sun kashe yan Boko Haram da dama tare da tserewa wasu da ciwuka masu matukar muni na gaske.

Jami’an dai sun samu bindigogin da mayakan Boko Haram suka gefar garin guduwa guda 4.

Haka zalika PRNigeria ta wallafa bidiyon yacce babban jami’in da ya jagoranci fatattakar yi wa wani babban kwamandan Soji bayani yadda abin ya faru.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00