//
Sunday, April 5

Kiru/Bebeji: Baza mu mara wa Kofa baya ba a zaben ranar Asabar -Dattijan APC

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Dan majalisar tarayya na Kiru da Bebeji wanda kotu ta soke zaben sa, Abdulmumin Jibrin Kofa ya shiga tsilla tsilla bayan da dattawan jam’iyyar APC ta jihar Kano suka ce sam bazasu goya masa baya ba.

Majiyar Dabo FM ta bayyana hakan ya fito cikin wani rahoto da jaridar PrimeTimes ta hada wanda ya tabbatar da dattawan jam’iyyar zasu yaki Kofa a zaben da za’a sake a mazabar Kiru da Bebeji ranar Asabar.

A ta bakin daya daga cikin dattawan ya bayyana cewa “Kofa bazai samu nasara a zaben da za’a sake na ranar Asabar ba, saboda muna zargin yana yiwa Kwankwaso aiki ne a cikin APC, don haka zamu kayar dashi.”

Masu Alaƙa  An samo wani mutumin Kano a raye bayan ya nutse a ruwa shekaru 30 da suka wuce

Bayan rikicin da ya barke tsakanin Abdulmumin Kofa da shugaban jam’iyyar APC ta jihar Kano, Abdullahi Abbas, a ranar Litinin da ta gaba ta majiyar mu ta hango dan majalisar a filin jirgin sama yaje taro shugaban jam’iyyar, wanda ya durkusa ya gaishe shi har kasa.

Bayan haka wakilan mu sun tabbatar mana da zuwan sa gidan gwamnati don yiwa gwamna murnar zabe, haka kuma hutunan sa tare da sanata Kabiru Gaya a garin Abuja, sai dai kuma ana ganin yana yin ladabin ne don ya samu goyan baya kara darewa kujerar sa.

Karin Labarai

Share.

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020