Home LabaraiKano Pillars ta lallasa Jigawa Golden Stars da ci 2 da nema

Kano Pillars ta lallasa Jigawa Golden Stars da ci 2 da nema

by Dabo Online
0 comments

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta lallasa takwararta ta jihar jihar Jigawa wato Jigawa Golden Stars da ci 2 babu ko daya a cigaba da bugun wasanni ajin Firimiya.

Wasan da kungiyar ta Kano Pillars ta buga a yau Lahadi, 15 ga watan Maris na 2020 a filin wasa na Sani Abacha dake jihar Kano ya kasance wasa na 24 da kungiyar ta buga a kakar bana.

Dan wasan kungiyar, Auwalu Ali Mallam ne ya jefa dukkanin kwallaye guda biyun inda ya fara jefa ta farko a bugun daga kai sai mai tsaron gida a minti na 29 kafin daga bisani ya jefa ta biyu a minti na 62.

Pillars tana mataki na 4 da maki 34 yayin da Jigawa Golden Stars dake kan mataki na 19 da maki 26.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00