Siyasa

Kalaman Ali Baba na ‘Sheikh Daurawa ba shi da ilimi’ sun janyo cece

Kalaman da mai bawa gwamnan Kano shawara a harkokin addinai, Ali Baba Agama Lafiya, yayi akan malamin addinin Islama, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, sun janyo cece kuce a tsakanin al’umma.

DABO FM ta tattara wasu daga cikin kalmomin da Ali Baba ya fada yayin wata hira da yayi a gidan Rediyon Express dake jihar Kano,

Ali Baba ya yace kalaman nasa a matsayin martanin gwamnatin Kano ne zuwa ga Shehin malamin bayan da yayi kira da yan majalissa da gwamnatin Kano suyi dokar abinda zai amfani mutanen Kano ba maganar tuhumar Sarki ba tin a wancen lokacin.

Ali yace; “Shi Daurawa, tin ranar da aka cire shi daga Hisbah, baya cikin hankalinsa. A masallaci yake yi wa mutane huduba, dan dai ka zama malamin fada, kace ‘yan Majalissa basa komai. Sarki ya kirawo ka bamusan me kuka ce ba, da kake cewa a cireshi ai da sai ka fada masa gaskiya.”

“Bazan kara jin karatun Daurawa ba don baya cikin malamai, dan siyasa ne tare muka zauna.”

Haka zalika Ali Baba ya bayyana Shehin malamin a matsayin wanda ya kirashi da “ba malami bane, bai ma yi karatu ba” hasa lima a cewarshi tambayoyin da yake amsawa a shirye-shiryen rediyo, “shine da kanshi yake tambayar kanshi.”

“Bari mu fada muku Daurawa ba malami bane, tambayoyin ma da yake amsawa a gidan rediyo ba mutane suke aiko da tambayoyin ba, shine yake rubuta abinshi daga gida kuma yazo ya bawa kanshi amsa.”

Ko da mai tambayar ta ce “tambayar da akwai mai karantowa daga sakonni mutane”, ya amsa da cewar “ai shi zai rubuto takardunsa ya bawa mai karantowar, in gaskiya ne ku hada shi kai tsaye mu mu tambayeshi.”

UA-131299779-2