0
A karon farko an a shekarar 2020 ruwan sama mai karfin gaske ya sauka a garin Zariya da ke Jihar Kaduna.
Ruwan da aka fara da misalin karfe 5:45 na yammacin yau Litinin, ya sauka a sassan daban-daban na garin harda makwaftar ta.
Dabo FM ta gano yanda wasu magudanar ruwa suka toshe saboda daukar lokaci ba tare da ruwa ya bi ta wurin ba.
A shekarar da ta gabata, garin Zariya ya fuskanci ruwa mai karfin gaske da ya jawo ambaliya a sassa daban-daban.
