//
Sunday, April 5

Gwamna a Indiya ya tilastawa jami’an Gwamnati hadawa marasa galihu kudin zaman gida

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Jaipur, India

Babban ministan jihar Rajasthan, Ashok Gehlot, ya baiwa kananan ministoci da ‘yan majalissun masu mulki a karkashin jami’iyyarshi ta Congress umarnin hada kudade domin ragewa marasa karfi radadin rashin fita neman na kai.

Kamar yadda ya bayyana a shafinshi na Twitter, Gehlot yace dukkanin jami’an gwamnatin zasu hada rupee dubu 100 (N520,000) domin baiwa al’ummar jihar.

Ministan ya bude asusun rage radadi mai taken ‘Rajasthan Chief Minister’s Relief Fund’ inda anan za’a tara kudaden.

DABO FM ta tattara cewar tin a ranar 22 ga watan Maris, gwamnatin jihar ta saka dokar hana fita domin kare yaduwar annobar cutar ‘Corona Virus’

Shugaban ya kara umartar ‘yan majalissun jihar dake a jami’iyyar Congress mai mulkin jihar da su bayar da albashinsu na wata daya domin tallafawa al’ummar jihar.

Masu Alaƙa  An fara kama matasan Arewa da Hodar Iblis a Indiya

Zuwa yanzu a kasar Indiya ta tabbatar da samun masu dauke da Corona Virus sama da 430.

Kasar ta rufe dukkanin makarantu har zuwa 31 ga watan Maris na 2020.

Karin Labarai

Share.

About Author

•Sublime of Fagge's origin. •PR Specialist •PharmD candidate

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020