Home LabaraiAlhaji Aminu Dantata ya bai wa jihar Kano Naira miliyan 300 don yakar Coronavirus

Alhaji Aminu Dantata ya bai wa jihar Kano Naira miliyan 300 don yakar Coronavirus

by Dabo Online
0 comments

Babban attajiri, Alhaji Aminu Alhassan Dantata, ya baiwa gwamnatin jihar Kano gudunmawar Naira miliyan 300 domim yaki da Coronavirus.

Alhaji Dantata ya bada gudunmawar ne ta kwamitin kafa asusun yaki da Coronavirus da gwamnati jihar Kano ta kafa a karshen makon da ya gabata.

Attajirin ya bayar da gudunmawar kudin a yau Litinin, kamar yadda kwamishinan yada labaran jihar Kano, Mallam Muhammad Garba ya bayyana a wata sanarwa da ya aikewa manema labarai.

Haka zalika sanarwar tace shugaban kamfanin Al-Amsad, Alhaji Abubakar Dalhatu da Alhaji Abba Sumaila sun bayar da gudunmawar katan din taliya 500 da Naira miliyan 5 kowannensu.

Muhammad Garba yace an samu gudunmawar farko tin bayan kaddamar da kwamitin daga bankin UBA da ya bayar da Naira miliyan 28.5, inda Alhaji Aliko Dangote ya alkauranta samar cibiya da kayyakin aiki cibiyar da zata kula da killace masu dauke da cutar Coronavirus.

Ya kara da cewar dukkanin kwamishinonin jihar da ma dukkanin jami’an gwamnati nadaddu zasu bayar da kaso 50 daga cikin albashinsu.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00