Sanatan Kano ta Arewa, Barau I Jibrin Maliya, ya baiwa gwamnatin jihar Kano gudunmawar Naira miliyan 4 domin yaki da cutar Coronavirus.
Haka zalika takwarorinsa guda biyu, Mallam Ibrahim Shekarau da Kabiru Ibrahim Gaya sun bayar da Naira miliyan 2 kowannensu.
DABO FM ta tattara cewar Sanatocin jihar sun bayar da kudaden ne zuwa ga asusun da gwamnatin jihar Kano ta bude domin yaki da Coronavirus, kamar yadda mataimakin gwamnan Kano a fannin yada labarai, Salihu Tanko Yakasai ya bayyana.
Hakazalika, yace sauran ‘yan majalissun wakilai dake jihar sun hada Naira miliyan dai-dai domin sakawa a cikin asusun taimakawar.
DABO FM tattara cewar Dattijo kuma attajiri, Alhaji Aminu Alhassan Dantata ya bai wa gwamnatin gudunmawar naira miliyan 300 duk dai domin yaki da cutar Coronavirus.
