A yayin da rabon kayan abinci da gwamnatin Jihar Kaduna ta samar ya shiga rana ta biyu a karamar hukumar Zariya, yanzu haka al’ummomin wasu anguwanni sun bayyana godiyar su ga gwamantin Jihar, saboda samar masu da kayan abincin da suka ce zai rage masu radadi a halin da ake ciki yanzu haka.
A cewar wasu mata da kuma mai Anguwar Kofar doka da suka zanta Dabo FM, sun bayyana yadda tsarin karbar kayayyakin zai kawo sauki a halin da ake ciki, inda suka gode ma Allah da kuma gwamnatin Jihar.
Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kaddamar da fara rabon kayan, shugaban kwamitin kula da rabon na karamar hukumar Alhaji Abdullahi Sani, ya ce zuwa yanzu sun karbi kusan dukkanin kayayyakin da al’umma za su amfana da shi, duk da akwai saura ‘yan kalilan da yanzu haka ke hanya. Daga cikin kayan da suka amsa akwai shinkafa da taliya da garin samobita da mangyada da kuma sauran su.
A wani labarin kuma rahotannin sun bayyana yadda aka samu musayar yamu da korafe-korafe daga wasu al’ummomin da ba’a sanya anguwoyin su ba cikin sunayen Anguwannin da za su amfana da kayan abincin, Anguwannin da suka hada da Albarkawa da Fada da Anguwan Magajin Aska da sauran su, Sun nuna takaicin su kuma suka ce watakila ko gwamnati ta manta da su ne.
Sai dai wani zagaye da Dabo FM ta yi, ya gano yadda wata kungiya da ke da manufar cigaban anguwar Magajin Aska suka samar da tsari na taimakawa marasa karfi a Anguwar da kayan hatsi kamar masara da wake da sauran su.
Shugaban kungiyar Kwamared Lawal Muazu, ya ce, akalla mutane 100 ne da ke ciki da kuma makwaftar anguwar ake sa ran za su amfana da rabon kayayyakin. Ya kuma bukaci gwamnati ta taimaka ta sanya su a sauran tsare-tsaren ta na gaba la’akari da dumbin al’ummar da ke cikin wannan Anguwa. Sannan ya nuna matukar godiyar sa ga masu hannu da shuni da suka taimaka da dukiyoyin su har aka samu nasarar shirin.
A wani labarin makamancin wanann kuma shirye-shirye sun yi nisa domin fara rabon kayan tallafin abincin a karamar hukumar Sabon gari, haka dai shugaban kwamitin kula da rabon Alhaji Umar Kabir Ibrahim ya shaidawa Dabo FM, ya ce, suna jiran raguwar kayan ne su iso, wanda kuma da zaran sun iso, suna sa ran a Litinin din nan rabon zai kankama.
