Koronabairas ta hallaka mutum na farko a jihar Kano

by Dabo Online
0 comments

An samu mutum na farko da ya rasa ranshi a jihar Kano sakamakon Koronabairas.

Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ce ta tabbatar da haka a shafinta na Twitter a wata sanarwa da ta fitar 11:55 na daren yau Laraba.

Ma’aikatar ta kuma tabbatar da samun mutane 12 da suka kamu da cutar, jumillar 21 cikin kasa da mako daya da bullar cutar.

Karin Labarai

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00