0
Hukumomin gudanarwar gasar Ligue 1 ta kasar Faransa ta soke gasar ta kakar 2019-2020.
Firaministan kasar Faransa, Edouard Philippe ya bayyana cewar kasar ta soke dukkanin al’amuran wasanni har zuwa watan Satumba.
Firaministan yace kasar ba za ta lamunci a cigaba buga wasanni ba duk da kafin a dena bugawa anayi babu ‘yan kallo.
Soke wasannin sun hada da dukkanin wasanni da ake gudanarwa a kasar da suka hada da gasar Rugby, Dambe da sauransu.
