Mutumin nan da ya fara kamuwa da cutar Koronabairas a jihar Kano, Amb Kabiru Rabi’u ya warke, har ma ta kai ga an sallameshi ya koma gida cikin iyalanshi.
DABO FM ta tattara cewar mutane sun yi ta cece-kuce tin a lokacin da aka bayyana mutumin ya kamu da cutar sakamakon an zarge ‘gaganci’ bayan shigowarshi Kano duk kuwa da ya san anyi masa gwajin cutar a birnin Abuja.
Da yake jawabi, shugaban yaki da cutar ta Kwabid-19 a jihar Kano, Tijjani Hussain ne ya tabbatar da hakan, inda yace sakamakon gwaji da aka sake yi wa Amb Kabiru Rabiu, ya nuna cewar ya warke daga cutar da ta abbadi duniya.
Kawo yanzu, da ranar yau Litinin, 11 ga watan Mayu, mutane 602 a jihar Kano, an kuma sallami mutum 50 inda kuma mutane 26 suka rasu, kamar yadda ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta tabbatar.
Bayan bayar da tallafin biliyan 4.3, Abdussamad BUA ya raba kayan abinci gida-gida a Kano
