Home LabaraiPantami ya dakatar da wani matashi daga yi masa ‘nasiha’ a Twitter

Pantami ya dakatar da wani matashi daga yi masa ‘nasiha’ a Twitter

by Dabo Online
0 comments
Pantami

Ministan Sadarwa na Najeriya Dr. Isa Ali Pantami, ya dakatar da wani matashi a shafinshi na Twitter bayan ya aike masa da sakon nasiha da jan hankali.

Ministan ya dakatar da matashi mai sunan @chachera88 a Twitter  ne ta hanyar yin ‘Blocking’ din shi ta yadda ba zai sake samun damar aika masa da wani sako ba.

Matashin ya aike wa Dr Pantami sakon tunasarwa kan yadda yace musulmai na rasa ransu a Najeriya ba tare da ministan ya yi abinda ya saba yi  na nuna damuwa da fada wa gwamnati gaskiya idan tayi kuskure.

Yace; In baka manta ba, ka taba yin karatu cewa duk wanda ya taba rike matsayin da ya kai minista a Najeriya sai ya shiga wuta. Sai gashi Allah ya jarabeka, a yau Kai minister ne.

Lokacin PDP ka taba fashewa da kuka sàboda yawan kashe kashe da ake. Amma sai gashi bayan an baka minista akwai ranar da saida aka kashe musulmi sama da 500 amma ko tak baka ceba balle kuka.”

Haka zalika ya ja hankalin ministan kan yadda yace ya na mai nuna gudun duniya, sai dai a cewar shi ya siyawa dan shi wayar N500,000 tare da sanya suturar da ta kai sama da N800,000 a jikinshi.

Ina zuwa karatunka a Abuja, kai da kullun kake nunama mutune su guji duniya, amma sai ga ‘danka yana rike wayar N500,000.

Kaima kanka daga hularka zuwa takalminka sunkai darajar N800,000. Na tabbata ba zaka kirga gida 20 ba daga gidanka na Gombe ba ba a samu Wanda ya kwana da yunwa ba.”

DABO FM ta tattara cewar matashin mai sunan @chachera88 a shafin Twitter, ya aike da sakon nasiha zuwa ga minista Dr Ali Isa Pantami da misalin karfe 11:44 na daren ranar 15 ga watan Mayun 2020.

Awanni 20 da mintuna 30 da aike sakon, Dr Isa Pantami ya haramtawa matashin sake aike masa sako ko bibiyarshi ta hanyar toshewar (Blocking) da Twitter ta tanada.

Ga cikakken sakon da matashin ya aike wa Dr Isa Ali Pantami.

“Nasiha zuwa ga
@DrIsaPantami

Bayan girmamawa irinta addinin musulunci. Allah ya gafarta mallam Ina kiranka da kaji tsoron Allah ka koma kan gaskiya.

In baka manta ba ka taba yin karatu cewa duk wanda ya taba rike matsayin da ya kai minista a Najeriya sai ya shiga wuta. Sai gashi Allah ya jarabeka, a yau Kai minister ne. Kuma lokacin PDP ka taba fashewa da kuka sàboda yawan kashe kashe da ake. Amma sai gashi bayan an baka minista akwai ranar da saida aka kashe musulmi samada 500 amma ko tak baka ceba balle kuka.

Sannan kuma, Ina zuwa karatunka a Abuja, kai da kullun kake nunama mutune su guji duniya, amma sai ga danka yana rike wayar N500,000. Kaima kanka daga hularka zuwa takalminka sunkai darajar N800,000. Na tabbata ba zaka kirga gida 20 ba daga gidanka na Gombe ba ba a samu Wanda ya kwana da yunwa ba.

Saboda haka ina Kira a gareka da kaji tsoron Allah. Bissalam. Daga masoyinka.”

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00