Home LabaraiShugaban limaman Juma’a na Kano, Sheikh Fadlu Dan Almajiri ya rasu

Shugaban limaman Juma’a na Kano, Sheikh Fadlu Dan Almajiri ya rasu

by Dabo Online
0 comments

Allah ya yi wa babban malamin addinin Islama, Sheikh Fadilu Dan Almajiri Fagge rasuwa yau Talata.

Kafin rasuwarshi, ya kasance shugaban limaman Juma’a na jihar Kano.

Malamin ya rasu ne a mahaifarshi ta Fagge, kamar yadda ‘yan uwanshi suka bayyanawa DABO FM.

A yanzu da karfe 9:30 na safe da muke hada wannan rahotan, mun samar sanarwar cewa za’ayi jana’izarshi a unguwar Fagge da karfe 1 na ranar yau kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00