Home Azumi24 ga watan Mayun 2020, Sallar Eid-el-Fitr – Sarkin Musulmai ya tabbtar

24 ga watan Mayun 2020, Sallar Eid-el-Fitr – Sarkin Musulmai ya tabbtar

by Dabo Online
0 comments

Mai alfarma Sarkin Musulmai, Abubakar Saad II ya tabbatar da rashin ganin watan Shawwal a fadin Najeriya, ya ayyana ranar Lahadi, 24 ga watan Mayu a matsayin ranar Sallar Idi karama.

Cikin sanarwar da Sarkin ya fitar mai dauke da sa hannun shugaban kwamitin shawari kan sha’anin addinin Musulunci, Farfesa Sambo Wali Junaidu, wazirin Sokoto.

“Kwamitin lura da ganin wata na kasa bai samu rahoto daga fadin Najeriya akan ganin jinjirin watan Shawwal na shekarar 1441 ba a ranar Juma’a, 22 ga watan Mayun 2020.”

“Don haka gobe Asabar, 23 ga watan Mayun 2020, itace ranar ga watan Ramadan na shekarar 1441.”

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00