RAJASTHAN: Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya amince da bude dukkanin kasuwannin jihar Kano.
Sai dai gwamnan ya ce za a bude kasuwannin ne a iya ranakun da gwamnatin jihar take daga dokar zaman gidan da ta sanya. Ranakun da suka hada da Laraba, Juma’a da kuma Lahadi daga karfe 6 na safe zua 6 na yamma.
Babban mataimakin gwamnan a fannin yada labarai, Salihu Tanko Yakasai ne ya sanar da haka yau Litinin cikin wani sako da ya wallafa a shafukanshi na sada zumunta.
DABO FM ta ttara cewar a yau Litinin ne gwamnatin tarayya ta sassauta dokar zaman gida da ta sanya a fadin jihohin Najeriya, in da ta bayyana dokar zaman gida ta koma daga karfe 10 na dare zuwa 4 na Asuba.
Kazalika ta baiwa gwamnonin jihohin Najeriya damar bude masallatai da coci-coci dake fadin jihohinsu.
Kalli yadda aka fafata tsakanin sojoji da ‘yan sanda a Zaria.
