Home Labarai12 ga Juni: Mun ciyar da ‘yan makaranta fiye da miliyan 9 -Buhari

12 ga Juni: Mun ciyar da ‘yan makaranta fiye da miliyan 9 -Buhari

by Muhammad Isma’il Makama
0 comments

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana gwamnatinsa ta ciyar da yara yan makaranta fiye da miliyan tara domin basu damar samun karatu mai inganci da basu abinci mai gina jiki.

Cikin sakon bikin ranar dumukuradiyya da DABO FM ta tattara daga cikin bayanin shugaba Buhari a ranar juma’a, shugaban ya bayyana cewa “A karkashin tsarin ciyar da yara yan makaranta mun ciyar da ‘yan makaranta 9,963,729 domin su zauna a makaranta tare da samun abinci mai gina jiki.”

Shugaba Buhari ya kara da cewa “A tsarin shirin N-Power kuwa mun dauki mutane fiye da dubu dari biyar (549,500), fiye da mutum dubu dari 4 wato 408,682 sun mori aika kudade na kaitsaye wanda ake kira da ‘Conditional Cash Transfer Programme.”

“A tsarin tallafin habaka sana’o’i kuwa fiye da mutum miliyan biyu sun amfana jimillar mutane 2,238,334, shirin da ake kira da ‘Growth Enhancement and Empowerment Programme’ a turance, baya ga mutane bila adadin da suka karu da shirin TraderMoni da MarketMoni.” Kamar yadda shugaban kasa ya bayyana.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00