Jaipur, India (DABO FM) – Gwamnatin tarayyar Najeriya ta amince da kashe da kashe Naira biliyan 13 domin kashe kwari a gonakin jihohi 12.
Jihohin da zasu amfana da kudaden sun hada da jihar Adamawa, Borno, Bauchi, Gombe, Jigawa, Kano, Katsina, Kebbi, Sokoto, Taraba, Yobe da Zamfara.
Ma’aikatar Gona da raya Karkara ce ta bayyana haka cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Najeriya ‘NAN’ ya rawaito.
A nashi bangaren, Ministan ma’aikatar, Alhaji Muhammad Sabo Nanono ya ce an ware kudaden ne domin tabbatar da kaucewa tsaiko a ayyukan noman shekarar 2020 a wadannan jihohin da za a kashe kudaden.
Ya kuma yi bayanin cewa za a yi amfani da wasu wajen kula da kwarin gona suke bakin haure wanda a cewarshi tini suka addabi arewacin da tsakiyar Afirika.
Ya ce za kuma a yi amfani da kudaden wajen rage tasirantuwar illar da cutar Kwabid-19 ta haifar tare da tabbacin samar wa da kasa abinci mai gina jiki.
Kazalika ministan ya nuna muhimmancin da gwamnatin shugaba Buhari ya ce ta bai wa bangaren noma kuma “za ta yi kokarin yakar dukkanin wani al’amari da zai kawo nakasu wajen cigaban bangaren noma.”
