0
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana baya dana sanin kirkirar masarautu da tayi sanadiyya yin tafiyar ruwa da rawanin Sarkin Kano na 14, Sanusi II.
DABO FM ta rawaito gwamnan ya fadi hakan ne a ranar Litinin cikin wani taron yan jaridu da ya gabatar a gidan gwamnati, wanda ya bayyana kirkirar masarautun na daya daga cikin aiyukan da yake alfahari dasu.
Ganduje yace “Sanusi ya rasa rawaninsa wajen kin bin sauyin da al’ummar Kano ke bukata, kuma masarautu na nan daram dam.”
Daga karshe Ganduje ya bayyana a yanzu an kori duk wata kara da take kalubalantar masarautun.
