Najeriya za ta samar da ayyukanyi 250,000 tare da samun kudin shiga na dalar Amurka miliyan 500 a shekara daya ta hanyar hakar gwal.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne ya bayyana haka jim kadan bayan karbar taron shaida kerarraren gwal na Najeriya na karon farko.
Cikin sanarwar da shugaban ya fitar ya ce yana fatan cigaban da aka samu yana da alaka da sauye-sauyen da gwamnatinshi ta yi kan dokokin hakar gwal a Najeriya.
“Sauye-sauyen sun bada kananan ‘yan kasuwa izinin hakar ma’adinai, wanda hakan zai bude wa kamfanoni hanyoyin sana’ar,” – Buhari
Masana sun bayyana cewar hakar gwal a Najeriya musamman a yankin arewa maso gabashin Najeriya na daga cikin abinda yake taimakawa yawaitar ayyukan ta’addancin ‘yan bindiga a kasar.
Buhari ya ce Najeriya ta rasa akalla biliyan 3 daga shekarar 2012 zuwa shekarar 2018 saboda masu hakar gwal ta haramtacciyar hanya.
