Home LabaraiYadda wasu ‘yan Zamfara su ke taimaka wa ‘yan Bindiga da masu satar Shanu

Yadda wasu ‘yan Zamfara su ke taimaka wa ‘yan Bindiga da masu satar Shanu

by Dangalan Muhammad Aliyu
0 comments

Alhaji Ibrahim Bello, Sarkin Gusau, ya zargi wasu ‘yan jihar Zamfara da taimakawa ‘yan bindiga, barayin shanu da masu garkuwa da mutane.

Sarkin ya ce wasu ‘yan jihar suna taimakawa ‘yan ta’addar ne ta hanyar sama musu gidajen haya da kuma siyar musu da gidajen da suke zama a ciki.

Sarkin ya bayyana haka ne yayin wani taro a ziyarar da babban sifetan ‘yan sandan Najeriya, Muhammad Adamu ya kai jihar ta Zamfara tare da darakta janar na hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, Yusuf Bichi.

Sarkin ya ce a ana samun ba ta gari da suke hada kai da ‘yan ta’addar wajen addabar al’ummar jihar, Sarkin ya ce sun gano haka ne bayan wasu tarurruka da suka gudanar.

Ya kara da cewa, ‘yan ta’addar kan kwana a cikin mutane amma da sassafe sai su fice zuwa inda suke aikata miyagun laifukansu.

Basaraken ya ce idan anyi amfani da bayanan asiri wajen gano wadannan batagarin da ke sayar musu da gidaje, zai taimaka wajen kama barayin da masu garkuwa da mutane.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00