Home LabaraiRikice-rikice: El-Rufa’i ya sanya dokar ta-baci a kananan hukumomin Jema’a da Kaura

Rikice-rikice: El-Rufa’i ya sanya dokar ta-baci a kananan hukumomin Jema’a da Kaura

by Dabo Online
0 comments
El Rufa’i

Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufa’i ya sanya dokar ta-baci a kananan hukumomin Kaura da Jema’a sakamakon rikici-rikici da suke faruwa a yankin.

Hakan na zuwa bayan neman da jami’an tsaro suka yi domin a fadada dokar ta-baci  zuwa kananan hukumomin biyu.

DABO FM ta tattara cewa kafin fadada dokar, akwai dokar a kananan hukumomin Kauru da Zangon Kataf.

Gwamnan ya sanar da sabuwar dokar a shafinsa na Twitter a jiya Juma’a.

A makon da ya gabata dai an samu karuwar rikice-rikice a yankunan Zikpak da Unguwar Masara.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00