Rashin Tsaro: ‘Yan Binduga sun sace Sifetan ‘yan Sanda a Adamawa

Karatun minti 1
"Yan BIndiga

‘Yan Bindiga a sun sace wani jami’in dan sanda mai mukamin Sifeta a garin Koma na karamar hukumar Jada a jihar Adamawa dake arewa maso gabashin Najeriya.

Kazalika ‘yan Bindugar sun sace wasu mata na wani fitaccen mafarauci da wasu mutane da jumillarsu ya kai 6.

Jaridar The Nation ta rawaici cewar; ‘Yan bindugar sun sace mutanen ne a yayin da suke cikin gidajensu da tsakar dare a ranar Alhamis ta makon da ya shude.

Rahotanni sun bayyana cewar ‘yan bindugar suna da mutanen da suke son sacewa domin bayan shigarsu garin a ranar Alhamis, sun bi gida-gida domin neman mutanen da suke nema wadanda basa zaune a kusa da juna.

A nata bangaren, rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar ta Adamawa ta hannun kakakinta, DSP Sulaiman Nguroje, ya tabbatar sace jami’in dan sandan tare da sauran mutane 6, ya bayyana cewa tini rundunar ta bi sahu domin kawo ‘yan bindugar.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog