Mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya za ta kashe kimanin Naira titiliyan 2.3 domin samar da hasken lantarki a kauyukan Najeriya a karkashin shirin Solar Home Systems (SHS).
Ya bayyana haka ne a cibiyar kasuwanci da masana’antu ta jihar Lagos ‘LCCI’.
Ya ce shirin zai samar da cibiyoyin sarrafa hasken wutar lantarki da gidaje miliyan 5 a fadin Najeriya.
Ya ce samar da kananun cibiyoyin zai sanya a kalla mutane miliyan 25 amfana da hasken lantarkin a kauyukan da suke fadin Najeriya gaba daya.
Ya ce, “Muna da zummar fara aikin da wuri, duba da cewa, sanya cibiyar sarrafa hasken ranar zuwa lantarki a gidaje miliyan 5 ba karamin aiki bane, dole a fara da wuri.”
A cewarsa, shirin zai taimakawa ‘yan kasuwa wajen bunkasa bunkasar kasuwancinsu tare da taimakawa kamfanunuwan magunguna musamman a irin wannan lokaci don samar da kayan yaki da cutar COVID-19.
