Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Kano ta sanar da fara tantance masu son shiga aikin dan sanda.
Hukumar ta ce za a tantance mutanen a Wuri Shedikwatar manyan ‘yan sanda ‘Officers Mess’ dake babbar Shedikwatar rundunar dake Bompai a birnin jihar Kano.
Da yake fitar da sanarwar, kakakin runduna, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce an fitar da ranaku da ‘yan kowacce karamar hukumar a fadin jihar Kano za su zo ofishin domin a tantancesu.
Ga dai yadda tsarin zai kasance;
SANARWA DAGA RUNDUNAR ‘YAN SANDAN JAHAR KANO 22/08/2020
YADDA ZA’A TANTANCE MASU SON SHIGA AIKIN ‘YAN SANDA A HELKWATAR ‘YAN SANDA DAKE BOMPAI KANO.
WURI: WAJEN SHAKATAWAR MANYAN ‘YAN SANDA (OFFICERS MESS), DAKE BOMPAI DA KARFE 0800 NA SAFE
- LITININ, 24TH AUGUST ,2020
AJINGI ALBASU BAGWAI BEBEJI - TALATA, 25TH AUGUST,2020
BICHI BUNKURE DALA DANBATTA - LARABA, 26TH AUGUST, 2020
DAWAKIN KUDU DAWAKIN TOFA
DOGUWA FAGGE - ALHAMIS, 27TH AUGUST, 2020
GABASAWA GARKO GARUN MALLAM GAYA - JUMA’A, 28TH AUGUST, 2020
GEZAWA GWALE GWARZO KABO - ASABAR, 29TH AUGUST, 2020
KANO MUNICIPAL KARAYE KIBIYA KIRU - LITININ, 31ST AUGUST, 2020
KUMBOTSO KUNCHI KURA MADOBI - TALATA, 1ST SEPTEMBER, 2020
MAKODA MINJIBIR NASSARAWA RANO - LARABA, 2ND SEPT, 2020
RIMIN GADO ROGO SHANONO SUMAILA - ALHAMIS, 3RD SEPT, 2020
TAKAI TARAUNI TOFA TSANYAWA - JUMA’A, 4TH SEPTEMBER, 2020
TUDUN WADA UNGOGO WARAWA WUDIL - ASABAR, 5TH SEPT, 2020;
WADANDA BASU SAMU DAMAR ZUWA A RANAKUN SU BA .
