Gwamnan Diffa ta jamhuriyar Nijar ya kai wa Zulum ziyarar jajen ‘harin Boko Haram’

Karatun minti 1
Gwamna Zulum da Gwamna Isa (Jihar Diffa) Nijar

Gwamnan jihar Diffa ta jamhuriyar Nijar ya kai ziyarr kwana 2 zuwa jihar Borno domin jajantawa Gwamna Babagana Umara Zulum bisa iftila’in da ya faru da shi a kwanakin baya a hanyar Baga.

Gwamnan Diffan Isa Lamin ya ce hakika a lokacin da suka ji labarin cewa ‘yan taddar Boko Haram sun kai wa ayarin motocin Gwamnan Borno hari, hankulansu sun tashi sosai, a cewarsa.

Ya ce jin hakan ya sa yayo tattaki domin yi wa gwamnan jaje tare da addu’a.

A nashi jawabin, gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum; ya ce tabbas jihar Borno da jihar Diffa tamkar Hasana ce da Husaina duba da yadda komansu guda Al’adunsu daya dan haka ko kadan bayyi mamakin zuwan tawagan yan jamhuyira Nijar ba, ya kuma ce hakika akwai yan gudun hijira da suke zama a jamhoriyar Nijar musan man a jihar Diffa kuma suna samun kulawa sosai daga Gwamnatin Isa lamin da ta Shugaban kasar Nijer.

Gwamna Babagana Umara Zulum yace zai hada karfi da karfe wajen yaki da ‘yan ta addar Boko Haram tare da daga martabar jihohin Borno da Diffa.

A ziyarar tasa Gwamna Isa Lamin na Diffa ya samu rakiyar Gwamnoni biyu daga yankin Nijer da ministocin Shugaban kasar Nijer da sauransu.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog