Home LabaraiKano Pillars ta lallasa Ifeanyi Ubah a birnin Fatakwal

Kano Pillars ta lallasa Ifeanyi Ubah a birnin Fatakwal

by Dabo Online
0 comments

Ƙungiyar Kano Pillars da a ke wa take da ‘Sai Masu Gida’ sun samu nasara a kan takwararsu ta Ifeanyi Ubah a yau Litinin a gasar Firimiya League ta Najeriya.

An tashi wasan  in da Pillars ta jefa ƙwallo ɗaya mai ban haushi a ragar Ifeanyi Ubah.

Wasan da aka buga a filin wasa na Adokiye Amiesimaka da ke birnin Fatakwal ya sa Pillars ta ɗare kan matsayi na 3 a kan teburin gasar.

DABO FM ta tattara cewar ɗan wasan ƙungiyar Pillars, Auwalu Ali Mallam ne ya jefa wa ƙungiyar ƙwallon a minti na 23. Ƙwallon ita ce ƙwallo ta da ɗan wasan ya ci a kakar bana.

Mutum 10,000 ne suka samu halartar wasan.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00