Home LabaraiTsofin Sojoji Sun Bukaci Gwamnati Ta Gaggauta Fara Biyan Sojoji Albashin N250k

Tsofin Sojoji Sun Bukaci Gwamnati Ta Gaggauta Fara Biyan Sojoji Albashin N250k

by Dabo Online
0 comments

Kungiyar tsofin sojojin Najeriya ta bukaci a gaggauta fara biyan sabon mafi karancin albashi na Naira dubu dari biyu da hamsin (N250,000) ga jami’an soji dake kan aiki a kasar.

Tsofin sojojin sun zargi Gwamnatin Tarayya da yin zagon kasa wajen aiwatar da dokar da Majalisar Tarayya ta riga ta amince da ita, kuma Shugaba Bola Tinubu ya sa wa hannu tun a karshen shekarar 2025.

Kamar yadda jaridar Punch ta bayyana, tsofin sojojin sun bayyana haka ne a ranar Litinin yayin wani taron tattaunawa da sama da tsofin sojoji 70 su ka halarta a ɗakin taro na ‘Armed Forces Headquarters Command Mess 1’ da ke birnin tarayya Abuja.

Babban Jami’in Tsaron Kasar (CDS), Janar Olufemi Oluyede, wanda aka sanya ran zai halarci taron, ya tura wasu manyan jami’an soji guda biyar su wakilce shi saboda tafiya da ya yi fadar shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu.

Ɗaya daga cikin masu shirya taron, Kanar Innocent Azubike (mai ritaya), ya bayyana cewa sun miƙa takardun shaidar da ke nuna amincewa da ƙarin albashin ga wakilan na CDS, kuma jami’an sun karɓa tare da yin alkawarin miƙa rahoton ga babban jami’in tsaron da zarar ya dawo.

Azubike ya bayyana ɓacin ransa kan yadda hukumomi suka yi gum da baki game da batun duk da alkawuran da a ka yi musu na watanni da dama. Ya bayyana cewa a watan Oktoban 2025, Majalisar Tarayya ta amince da kudirin dokar duba albashin sojoji bayan wani bincike ya nuna cewa albashin sojojin Najeriya ne mafi kankanta a cikin kasashen Afirka da dama.

Ya kara da cewa, Shugaba Tinubu ya sanya wa kudirin hannu a watan Nuwamban 2025 tare da bayar da umarnin cewa a aiwatar da shi tare da biyan tulin albashin na baya (arrears) na tsawon watanni uku.

Sai dai tsofin sojojin sun yi mamakin yadda hukumomin tsaro a wannan watan na Yuli 2026 suka fara nuna kamar ba su da masaniya kan wannan karin albashi, inda suke neman tsofin sojojin da su kawo takardun shaida.

A karshe, Kanar Azubike ya nanata cewa tsofin sojojin suna nan daram kan shirin gudanar da zanga-zangar lumana a Ma’aikatar Kudi ta Tarayya domin neman hakkinsu, muddin hukumomi ba su dauki mataki cikin hanzari ba.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00