Home LabaraiBuhari ya bada umarnin daukar matakin kuɓutar da Zainab Aliyu dake tsare a ƙasar Saudiyya

Buhari ya bada umarnin daukar matakin kuɓutar da Zainab Aliyu dake tsare a ƙasar Saudiyya

by Dabo Online
0 comments

Shugaba Muhammadu Buhari ya baiwa Ministan Shari’a, Abubakar Malami SAN umarnin bin diddigi tare da daukar matakin daya dace akan lamarin Zainab Aliyu, yar jihar Kano da aka tsare a kasar Saudiyya bisa shiga da kwaya zuwa kasar.

Babbar mai baiwa shugaba Buhari shawara akan harkokin kasashen waje, Abike Dabiri Erewa ce ta bayyana haka a shafinta na Twitter yayi da take mayar da martani akan kiran da matasa sukayi a Twitter domin neman gwamnatin ta shiga maganar.

“Muna aiki hakan batun. Tin makonni 2 da suka wuce, Shugaba Buhari ya baiwa Attorney General umarnin daukan dukkan matakin daya dace. Muna samu cigaba akan aikin, ita (Zainab ALiyu) dama sauran mutum 2 da suka tsinci kansu a irin lamarinta, zasu dawo gida.”

A yan kwanakin nan ne dai hukumomi a kasar Saudiyya suka cafke Zainab Aliyu a kasar Saudi Arabia bisa kokarin shigar da miyagun kwayoyi zuwa kasar.

Hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da hukumomin Saudiyya suka fillewa wata ‘yar Najeriya kai bisa kamata dumu-dumu da kwayoyi.

Sai dai bayan bincike da hukumar NDLEA ta gudanar a Najeriya, ta samu nasarar cafke wasu ma’aikatan Airport da laifin saka kwayoyi a cikin jakunkunan matafiya daga Najeriya.

Hakan yasa yan Najeriya suke tashi musamman matasa wajen fafutukar gwaamnati ta shiga lamarin wajen kubutar da ‘yan Najeriyar da aka kama a kasar Saudiyya bisa la’akarin da cewa dukkaninsu a saka musu kwayar ne batare da saninsu ba.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00