Zababben dan majalissar tarayya da wata kotu ta kwacewa kujera, Hon Abdurrahman Kawu Sumaila, ya kaddamar da fara tafsirin azumin Ramadan na bana.
Tsohon babban mai bawa shugaba Buhari shawara a harkokin majalissar tarayya, ya bude karatun ne jiya a garin Sumaila dake jihar Kano.
Hon Kawu Sumaila yayin gudanar da Tafsiri
A makonnin da suka gabata ne dai wata kotu ta kwace kujerar wakilcin karamar hukumar Takai/Sumaila daga hannun Kawo bisa tabbatar da rashin fafatawarshi a zaben fidda gwani da akayi a jami’iyyar su ta APC.
Kawu dai ya nemi tsayawa takarar Sanata, inda ya kara da Sanata Kabiru Ibrahim Gaya.