Gobe Litini, za a tashi da azumin Ramadana a kasar Saudi Arabia

Karatun minti 1

Kamfanin Dillancin Labarai na kasar Saudi Arabiya, SPA, ya rawaito cewa hukumomi a kasar Saudiyya sun bada tabbacin daukar azumin watan Ramadan daga gobe Litinin.

Kamfanin yace “An ga jinjirin watan Ramadan a 2019 a kasar Saudiyya.

Masu duban watan dake Hotat Sudair sun tabbatar da ganin jinjirin watan Ramadhan na shekarar 1440AH.

Tuni dai babbar kotun kasar ta bada sanarwar gobe Litinin, shine 1 ga watan Ramadan tare da aike sakon murnar ta ga masaurautar kasar ta Saudiya dama daukacin al’umma musulimin duniya baki daya.

“Kamar yadda annabi Muhammad (SAW) yace mu dauki azumi tare da sauke shi bayan munga wata, babbar kotu kasar ta yanke ranar Litinin daya ga watan Ramadhan na shekarar 1440AH wanda yayi daidai da ranar 6 ga watan Mayun 2019.”

SPA

Karin Labarai

Sabbi daga Blog