A shirin aurar da Zaurawa wanda gwamnatin jihar Kano ta gada daga gwamnatin da ta shude, yau ma gwamnatin jihar karkashin jagorancin Dr Abdullahi Umar Ganduje ta aurar da zawarawa mata da maza guda 3000.
An dai daura auren guda 70 daga cikin 1,500, a babban masallacin jihar Kano na gidan Sarkin dake karamar hukumar Birni a kwaryar garin Kano.

Daurin auren na masallacin Sarki , ya samu halartar manya-manyan mutane wadanda suka hada da Gwamnan jihar Dr Abdullahi Umar Ganduje, Mai martaba Sarkin Kano, Mallam Muhammad Sunusi na biyu.

Shugaban Jami’iyyar APC na jihar Kano, Hon Abdullahi Abbas da sauran mukarraban gwamnatin su samu halartar daurin aure.
Hotunan daurin auren a karamar hukumar Fagge, inda aka daura a babban masallacin Juma’a dake unguwar ta Fagge.
Daurin auren na Fagge, ya samu halartar shugaban karamar hukumar Hon. Shehi, Na’ibin limamin masallacin Waje, Mallam Sa’id Na’ibi.

Aurar da zaurawa yana daga cikin ayyukan da tsohon gwamnan jihar, Engr Kwankwaso ya fara, inda ya aurar da kusan ma’aurata 10,000 tsakanin shekarar 2013-2014.



