A kwanaki 105, CP Singham ya gurfanar da masu laifuka sama da 3000 a gaban Kotu

Kwamishinan mai ritaya, CP Muhammad Wakili yayi ritaya daga aikin ‘dan sanda a ranar Juma’ar 26/05/2019.

Ritayar Singham tazo ne bisa cikarshi shekaru 60 a duniya.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kano, DSP Haruna Abdullahi ya bayyana haka a shafinshi na Facebook.

“Zamansa a kano na kimanin kwanaki dari da biyar (105) ya gurfanar da sama da mutane 3000 a gaban kotu abisa aikata laifukan daba da shan kwaya.

“Ya taka rawar gani wajen kare lafiyar al’ummar jihar kano da dukiyoyinsu musamman lokacin zaben 2019.”

%d bloggers like this: