Labarai

A najeriya, an haifi Jarirai sama da 26,000 a daren sabuwar shekarar – UNICEF

Asusun Kula da Kananan Yara na Majalissar dinkin Duniya, UNICEF ya bayyana cewa Najeriya zata samu Jarirai sama da 26,039 a daren sabuwar shekarar 2020.

Asusun yayi kiyasin cewa za’a haifi yara kimanin 392,078 a fadin duniya, UNICEF ta kuma sanya kasar Indiya a matsayin kasar da za’a fi haihuwar Jarirai wanda adadinsu ya kai 67,385.

UNICEF tace kasar China ke biye wa Indiya baya da Jarirai 46,299, Najeriya ta zama ta uku da samun Jarirai 26,039.

Kasar Pakistan kuwa, za’a samu 16,787, kasar Indunusiya, za’a samu 13,020 yayin da kasar Amurka za’a samu Jarirai 10,452, Jamhuriyar Congo za’a samu 10,247 tare da kasar Habasha, za’a samu Jarirai 8,493.

UNICEF tayi hasahen fara samun Jaririn farko a nahiyar Pacific inda kuma tace za’a samu na karshe a kasar Amurka.

DABO FM ta tattaro cewa wakilin UNICEF a Najeriya, Peter Hawkins ne ya bayyana haka a wata sanarwa daya raba wa manema labarai a birnin tarayyar Abuja.

Ya kuma yi tunasar da gwamnati akan kulawa da duk wani yaro a Najeriya domin gudanar da rayuwarshi cikin kulawa da walwala.

Karin Labarai

Masu Alaka

Tsakani da Allah har yanzu ba’a fara aikin Wutar Mambila ba – Ministan Lantarki

Dabo Online

Nima na cancanci samun kyautar wanzar da zaman lafiya ta ‘Nobel Prize’ -Buhari

Muhammad Isma’il Makama

Ba mu ba APC – Rochas

Dabo Online

‘Fasa Kwauri’ ya karu duk da rufe iyakokin Najeriya

Dabo Online

Gwamnatin ta sake jaddada kudurinta na fitar da ‘Yan Najeriya miliyan 100 daga talauci

Dabo Online

Buhari yayi Allah wadai da dage zabe

Dabo Online
UA-131299779-2