//
Wednesday, April 1

Yanzu Yanzu: Gwamnan Bauchi ya bada umarnin biyan sabon albashi na N30,000

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad Kauran Bauchi ya bada umarnin biyan mafi karancin albashi na N30,000 ba tare da wani bata lokaci ba duk da rashin cimma matsaya tsakanin gwamnatin da kungiyar Kwadago

Sai dai gwamnatin zata bawa ma’aikata masu matakin 01 zuwa 07 kacal.

Dabo FM ta tabbatar da sanarwar ta bakin kwamishinan kasafin kudi da tsare tsare na jihar, Malam Aminu Gamawa.

Gamawa ya bayyana cewa ” Gwamna Bala Muhammad ya karbi rahoton biyan sabon albashi mafi karancin na naira dubu 30, kuma ya bada umarni fara biyan nan take.”

Ya kara da cewa “Za’a fara biyan ne daga gobe 1 ga Junairun sabuwar shekarar 2020.”

Masu Alaƙa  Duk shifcin-gizo gwamnoni keyi a batun biyan Sabon Albashi -Kungiyar Kwadago

Sai dai har yanzu an gaza cimma matsaya tsakanin bangaren gwamnatin da kungiyar Kwadago akan biyan albashin.

Tsagin gwamnatin ya bayyana zasu fara biyan ma’aikata dake a matakin 01-07 a wannan lokacin inda daga bisani su fara biyan masu matakin sama da haka da a hankali.

Ita kuma a bangarenta, Kungiyar Kwadago ta teshen jihar Bauchi, taki amincewa da biyan masu matakin 01-07 kadai.

Andai tashi taron ba tare da an cimma matsaya tsakanin bangarorin biyu ba.

Karin Labarai

Share.

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020