Zamfara: Gishirin Lalle yayi sanadiyar mutuwar mutum 14

Kimanin mutum 14 ne suka mutu a kauyen Moda ‘Karamar Hukumar Anka dake Jihar Zamfara.

Mazauna ‘kauyen sun shaidawa manema labarai cewa wata matar gida ce ta zuba Gishirin Lallen a rashin sani cikin miyar da take dafawa, a daukar ta garin dandano ne na Ajino Moto.

A ta bakin wani ma’aikaci na Karamar Hukumar, yace “Duk wadanda suka ci abincin sun riga mu gidan gaskiya, 8 daga ciki sun rasu ne a asibiti kusa da garin Sokoto, sauran 6 kuma sun rasu a gida.”

Ya kara da cewa “Kasan a al’adar hausawa idan anyi abinci ana fito dashi kofar gida makwafta da ‘yan gida suci, abin ta’ajibi kusan kowa da yake wajen yaci abincin wanda duk wanda yaci gubar ta kashe shi, a ciki harda matar data dafa da wasu mata 4, a ciki mutum 8 ‘yan gida daya ne, cikin ikon Allah uwar gidan da mijin sun tsira da ransu, dan basa gida sanda abin ya faru, inda tini ma an binne mamatan.”

Masu Alaƙa  Kisan Kolade Johnson abin baƙin ciki ne ƙwarai da gaske - Shugaba Buhari

Mai magana da yawun Hukumar ‘Yan Sanda, SP Muhammad Shehu, ya tabbatar da faruwar lamarin, saidai yace rahoton su mutum 8 ne suka rasu, amma suna ci gaba da bincike.

Karin Labarai

Leave a Reply

Your email address will not be published.