Labarai

Kungiyar ‘Yan Jaridu ta mika Ta’aziyyar rashin Ma’aikacin NTA

An bayyana rashin Marigayi Malam Hashimu Adamu, Ma’aikacin Tashar Talabijin na Kasa NTA Zaria, a matsayin babbar rashi ba ga kafar yada labarai ta NTA ko iyalan sa ba, rashi ne ga al’umma baki daya.

Shugaban Kungiyar ‘Yan Jarida ta Kasa shiyyar Zaria Kwamared Bello Habib, ya bayyana hakan, sa’ilin da yake mika sakon ta’aziyyar sa, ga Iyalai ‘Yan uwa da kuma abokan arziki na Hashim Adamu.

Ya kwatanta shi, a matsayin mutum mai natsuwa da kame kai da kuma haba-haba tsakanin abokan aikin sa, musamman lokacin da yake gudanar da aiki.

Ya naimi sauran ‘Yan Jaridu, su yi koyi da halayyan sa domin samun rayuwa mai kyau kuma abun kwatance.

Daga nan, sai Shugaban Kungiyar ‘yan Jaridan, ya mika sakon ta’aziyyar sa a madadin Kungiyar shiyyar Zaria, ga iyalai, ‘yan uwa da kuma Hukumar Tashar Talabijin na Kasa NTA, kuma ya roki Allah Rahimin Sarki ya gafarta masa kura-kuren sa.

Karin Labarai

Masu Alaka

Jaafar Jaafar ya rasa mahaifiya

Dabo Online

Mahaifin Hafsat Idris ‘Barauniya’ ya koma ga Allah

Dabo Online

An binne dan Najeriya da ya rasu a kasar Indiya bisa koyarwar addinin Musulunci

Dabo Online

Jigawa: Dan Majalissar Tarayya ya sake rasuwa

Dabo Online

An binne Dalibin da ya rasu jim kadan bayan kammala Digirinshi na 2 a kasar Indiya

Dabo Online

Sarkin kasar Oman, Qaboos bin Said ya rasu bayan shekaru 50 kan mulki

Dabo Online
UA-131299779-2