Labarai

Abin Yazo: Lahadi, 21 ga Afirilu, Za’a Daura auren Abba da Rufai’atu

Bayan baiko da akayi na yaronan nan Abba, mai shekara 17 da Amaryarshi Rufai’atu, mai shekara 15.

Katinan daurin auren sun bayyana inda aka tsara daura auren a gobe Lahadi, 21 watan Afirilun 2019 da misalin karfe 11 na safe.

Tin bayan samun labarin auren Abba da Rufa’atu, al’umma Najeriya, kudu da arewa sukayi ta tofa albarkacin bakinsu akan lamarin.

Inda wasu ke ta san barka da jin zancen kuma sukan yi togashiya da cewa hakan shine yafi dacewa ga mutane musamman a yanayi da ake ciki na gurbacewar matasa.

Suma wasu a nasu bangaren suna ganin bai kamata ace a aurar da yara irinsu a wannan lokacin da suka kira basu gama sanin menene auren bama ballanatana muhimmancin shi.

Malamai dayawa musamman na addinin musulunci sun bayyana wannan aure a matsayin Abinda ya a dace  al’ummar musulmi.

Sunce hakan zai taimaka wajen rage zinace zinace dake faruwa a ban kasa a cikin wannan zamani.

Daga bangare wasu wadanda mafi yawansu mazauna kasashen turai su kuma nasu ganin ya sha bambam, inda suke ganin kamar anci zarafin yaran baki daya.

Suna ganin za’ayi auren ne bisa tursasawar iyayen yaran.

Karin Labarai

UA-131299779-2