Malaman Jami’a su dena shiga harkokin Zabe domin ceton Ilimi

Shehu Sani, sanatan Kaduna ta tsakiya, yayi kira da a hana malaman jami’a shigar harkokin zabe.

A Najeriya dai hukumar zabe ta INEC tana daukar malaman jami’o’i aikin wucin gadi a lokacin gudanar da zabe a kasar.

Sanata Shehu Sani yayi wannan kira ne a shafinshi na Twitter jim kadan bayan wasu maganganu da akaji tsohon shugaban hukumar zabe, Prof Attahir Jega yace anyi amfani da malaman jami’a wajen yin magudi da murdiya a zaben 2019.

Ya kara da cewa, cire malaman daka sabgar zabe zata cigaba da daga martabar malaman da kuma jami’o’in.

 

%d bloggers like this: