Home LabaraiYanzu- Yanzu: Sarki Sunusi ya karbi nadin Ganduje

Yanzu- Yanzu: Sarki Sunusi ya karbi nadin Ganduje

by Dabo Online
0 comments
Muhammadu Sunusi II

Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II, ya karbi nadin gwamnan Kano, Ganduje a matsayin sabon shugaban Majalissar sarakunan jihar Kano.

Hakan na zuwa ne bayan wa’adin kwana 2 da gwamnan ya bawa Sarki Sunusi wanda ya fara daga jiya, 19 ga Disamba.

Takardar da babban sakataren masarautar Kano, Abba Yusuf ya sanya hannu ta shaida karbar nadin da gwmnan yayi wa Sarkin Kano ta tabbatar da aiwatar da umarnin gwamnan akan nadin yan majalissar.

Takardar da DABO FM tayi ido hudu da ita ta bayyana kanta a matsayin karbar nadin da kuma jiran umarnin gwamna Ganduje akan nada sauran yan Majalissar.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00