//

Wa’adin da Ganduje ya bawa Sarki Sunusi na karbar shugabancin Majalissar Sarakuna zai kare gobe

0

Ranar 21 ga watan Disamba, wa’adin da Gwamnatin jihar Kano ta bawa Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II, na rubuto mata takardar karbar shugabancin Majalissar Sarakunan jihar Kano da gwamnan jihar ya bashi, zai kare.

Hakan na kunshe a jikin wata takarda mai lamba SSG/SD/A/36/S/T.III da gwamnatin ta aikewa Sarkin Kano ta ofishin sakataren gwamnatin jihar a ranar 19 ga watan Disamba wacce DABO FM ta ganewa idanuwanta.

Gwamnatin ta yi wa mai martaba Sarki tini kan bukutar gwamna na ya rubutu shaidar ya karbi mukamin, ko kuma rashin karbarshi.

Takardar tace; “A yanzu da kake jiran wani tsammani daga gwamna, yana da kyau ka karbi nadin ko kuma sabanin hakan.”

Masu Alaƙa  Muna aiki ta karkashin kasa domin sasanta Sarki Sanusi da Ganduje -Shekarau

“Ana bukatar ka aikewa matsayarka kan nadin da akayi cikin kwana biyu daga ranar da aka aiko maka da wannan takardar.”

DABO FM ta tattara cewa tin dai a ranar 9 ga watan Disamba, gwamna jihar ya nada Sarkin Kano a matsayin sabon shugaban Majalissar Sarakuna tare da umartarshi da ya aike da rubutaccen sakon karbar mukamin da gwamnan ya bashi.

Haka zalika ya kuma hada taro ya rantsar da sauran sabbin ‘yan Majalissar wadanda suka hada da sabbin Sarakunan Kano guda 4.

Duk dai a takarda mai lamba SSG/REPA/S/A/86/T, gwamnan ya bawa Sarki Sunusi damar kin karbar nadinshi a matsayin shugaban Majalissar.

A jiya Alhamis, gwamnan ya bayyana yacce wasu kungiyoyin yan kishin jiha suna bukaci a tsige shi bisa yunkurinshi (Sarki Sunusi) na kirkirar sabuwar jihar Kano.

Masu Alaƙa  Galadiman Kano ya cika shekara biyar da rasuwa

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
©Dabo FM 2020