(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Abuja: Wata Mata ta rafke mijinta da falankin katako har lahira

dakikun karantawa

An zargi wata uwargida mai suna, Bilkisu Isah, da kashe mijinta biyo bayan wani dan sabani tsakaninta da mijinta, Isah Egba, a babban birnin tarayyar Abuja.

Lamarin ya faru ne a unguwar Sabon Tasha dake birnin Abaji, Abuja, kamar yadda jaridar Daily Trust ta tabbatar.

DAILY TRUST tace wani makocin ma’auratan mai suna Salihu ne ya bada shaidar faruwar lamarin.

DABO FM ta rawaito Salihu ya ce, Al’amarin ya faru ne a ranar Alhamis da misalin karfe 9:12 na dare bayan samun sabani mamacin da matar ‘ya ‘yanshi guda 5.

Yace lamarin ya faru ne sakamakon ficewarta daga gida bada izininshi ba kuma tayi dadewar da sai kusan karfe 8 na dare ta koma gida.

Kamar yacce Salihu ya bayyana, Mijin Bilkisu ya janyo ta tare da umarnin ta fice masa daga gida, lamarin daya bata mata rai har ta harzuka ta dauki falakin katako a jibga masa a kai.

Take a wajen mutumin ya fara zubar da jini, wasu makota suka hanzarta wajen kaishi asibitin Abaja Comprehensive Health Centre inda taga bisani aka mayar dashi asibitin koyarwa na jami’ar Abuja a Gwagwalada, sai dai a tsakar daren Juma’a yace ga garin kunan.

Bincike ya nuna cewa Isah, yana aiki da ma’aikatar kudi ta karamar hukumar Abaji.

Tini dai aka riga aka binne mamacin bisa yacce addinin musulunci ya tanada a makabartar musulmai dake karamar hukumar Abaji a birnin Abuja.

DSP Anjuguri Manzah, na rundunar ‘yan sanda mai kula da unguwar Abaji, ya tabbatar da faruwar al’amarin, kuma ya kara da suna ci gaba da bincike.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog