Labarai

Akwai yiwuwar Najeriya ta sake komawa cikin matsin tattalin arziki ‘Recession’ – CBN

Gwamnan babban bankin kasa, Godwin Emefiele ya bayyana cewa Najeriya za ta iya kara komawa kangin matsin tattalin arziki idan ba’a dauki matakin gaggawa wajen samar da ayyukan yi a kasa ba.

Emefiele ya bayyana haka ne a yayin da yake gudanar da lakcha a jami’ar Benin mai taken “Kiddidigar kudade bisa rashin tabbas.”

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Gov Emefiele yace dole ne a fara tunanin daukar mataki domin dakile komawar kasar cikin matsin tattalin arzikin.

“In kun lura a cikin maganganu na, dole ne a san cewa akwai matsaloli na rashin tabbas akan kudaden duniya wanda akwai tabbacin zai iya kaiwa ga wata matsalar babba.”

“Dole ne mu tambayi kanmu, a matsayinmu na ‘yan Najeriya, musamman ga shuwaganninmu, tayaya muke shirin tarar barkewar wata barakar tattalin arziki?.

DaboFM ta tatataro Emefiele yana cewa; “Munyi sa’ar fita daga cikin wani matsin. Mun samu raguwar matsin tattalin arziki akalla da kaso 18.72 a shekarar 2017 zuwa 11.37 da muke ciki a yau.  Asusunmu yana kara habbaka, kudinmu yana samun tsayayyar daraja, sai dai har yanzu akwai kalubale da yake tunkararmu akan rashin ayyukan yi. 

Gwamnan ya bada tabbacin cewa babban banki zai cigaba da kokartawa wajen yin duk mai yiwuwa wajen taimakon fidda kasar daga komawa wani matsin na tattalin arziki.


Karin Labarai

Masu Alaka

N30 kacal Banki zai caji wanda ya cire N501,000 a asusun Banki -CBN

Dabo Online

Bankin CBN ya ja kunnen Buhari akan yawaitar ciyo wa Najeriya bashi

Muhammad Isma’il Makama

N20 kacal Banki zai caji wanda ya sanya ko cire N501,000 a asusun Banki -CBN

Dabo Online

Majalissar Dattijai ta tabbatar da sake nada Emefiele a matsayin gwamnan CBN bisa kudirin shugaba Buhari

Dabo Online

CBN zata dauki dukkanin ‘yan jihar Ebonyi masu matakin ‘First Class’ a Economics aiki

Dabo Online

Ingantattun hanyoyin kaucewa biyan sabon cajin kudin Banki da CBN ta kakaba

Dabo Online
UA-131299779-2