Copyrighted.com Registered & Protected

Kano: Wadanda babu zargin cin hanci da rashawa akansu ne zasu zama kwamishinoni – Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje yayi jawabin bankwana da shuwagabannin ma’aikatan jihar Kano tare da kwamishinonin jihar a kwanaki da ya rage kasa da mako guda wa’adin mulkin gwamnan ya kare.

DaboFM ta tattaro jawabin Gwamnan dai dai lokacin da yake ganawa da ‘yan majalissar zartarwa na jihar Kano a zaman da yayi dasu na karshe a wa’adin mulkin jihar da ya fara a shekarar 2015.

Ganduje ya bayyana jin dadinshi da godiya ga sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Usman Alhaji bisa jajircewarshi a tafiyar da mulkin jihar.

“Sakataren gwamnati muna godiya, anyi aiki tukuru, sosai da sosai, komai ya tafi dai-dai, banyi mamaki ba saboda kana da kwarewa a aiki na gwamnati.

DGanduje ya godewa shugaban ma’aikata tare da yaba masa kan yacce ya rike kungiyar kwadago har aka kammala shekaru 4 ba tare da samun babbar matsala da ma’aikatan jihar ba.

Masu Alaƙa  An nada Sarakunan Kano da kyakkyawar niyya ne, ba abinda zai rushe su - Ganduje

Gwamnan godewa kwamishinoni tare da yaba kan yacce gwamnan yace har suka gama ba’a taba samun wani da zargin cin hanci da rashawa ba.

“Ina gode muku, har muka gama, ba’a zarge ku da cin hanci da rashawa ba, ba’a zargemu da nuna bambanci wajen sarrafa ma’aikata. Wannnan  ba karamin kokari bane.

Gwamnan yace dole ne su tantance wadanda zasu kara baiwa aiki a jihar Kano, dole sai wanda yake mai amana tare da zama mai biyayya ga gwamnan, haka zalika wanda bai zai ci hanci da rashawa ba.

Daga karshe gwamnan ya gode musu akan yacce sukayi tsayuwar tsayin daka wajen zabe, musamman wadanda suka yi bajinta lokacin da hukumar INEC tace zaben jihar bai kammala ba.

Masu Alaƙa  Buhari bai shiga maganar sasanta Ganduje da Sarkin Kano ba - NTA

Masu alaka

Bayyana ra'ayi a sahafinmu na Facebook

Gargadi

Ba'a yarda wani kamfanin Labarai ko shafi yayi amfani da Rahotanninmu ba tare da tuntubarmu ba. Tuntube mu ta "submit@dabofm.com
%d bloggers like this: