Mon. Nov 18th, 2019

Dabo FM Online

World’s First pure Hausa online Radio

Kashi 18 daga cikin 30 na masu tabin hankali a Najeriya, Mata ne – Likitan Kwakwalwa

1 min read

Bisa binciken da Dr Auwal Sani Salihu na asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano dake jihar Kano ya gudanar, Dr Auwal yace kaso 6 daga cikin 10 na matan Najeriya suna da tabin hankali, inda suk kuma maza suke da kaso 4.

DaboFM ta tattaro cewa; Daga cikin adadin 60,300,000 na masu tabin hankalin na Najeriya, 36,180,000 daga cikinsu Mata ne, 24,120,000 Maza.

Mata suke da kaso 18, Maza kuma nada 12 daga cikin kaso 30 na ‘yan Najeriya masu tabin hankali.

“Ciwon Hauka a Najeriya yana karuwa sosai. Mutane suna kara samun tabin hankali bisa wahalhalun da ake fama dashi a kasar nan. Basu da kudi, mutane da dama suna fadawa shan magani ba tare da umarnin masana na ba. Mutane dayawa suna yiwa giya shan ganganci da ta’ammali da miyagun kwayoyi irinsu Tramol da tabar wiwi.

Daga bakin kwararren likitan kwakwalwa na Asibitin Koyarwa na jami’ar Ilorin, Dr Baba Issa.

Gargadi

Ba’a yarda wani kamfanin Labarai ko shafi yayi amfani da Rahotanninmu ba tare da tuntubarmu ba. Tuntube mu ta “submit@dabofm.com©2019 Dabo FM Online. Sponsored by Dabo Media Group | Newsphere by AF themes.