Abdulaziz Yari ya mikawa Matawalle takardun mulkin jihar Zamfara

Gwamnan jihar Zamfara mai barin gado, Gwamnan Abdulaziz Yari ya bawa Bello Muhammad Matawalle, zababben gwamnan jihar, takardun kama aiki a yau Laraba, 28/05/2019.

Ana sa ran rantsar da sabon gwamnan a gobe Alhamis, 29 ga watan Mayu, 2019 kamar yadda dokar Najeriya ta shirya.

Nasarar Matawalle da zo ne bayan da babbar Kotun koli ta ruguje ‘yan takarkarun jami’iyyar APC ciki hadda ‘dan takarar gwamnan jihar ta Zamfara.

Hakan yasa jami’iyyar APC ta rasa dukkanin kujerar mulki a jihar Zamfara.

DaboFM ta tattaro cewa; jami’iyyar APC ta lashe dukkanin mukaman mulkin a jihar, kafin daga bisani kotu ta ruguje su bisa rashin gudanar da zaben fidda gwani a jami’iyyar.

%d bloggers like this: