Allah Ya’azurtani da samun ‘Ya’ya 70 da tarin Jikoki – Sheikh Dahiru Bauchi

Babban Malamin addinin Islama a Najeriya, mataimakin shugaba a Kwamitin Fatawa na Najeriya, Jagoran darikar Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya bayyana cewa yana da ‘ya’ya guda 70 tare da tarin Jikoki.

DABO FM ta binciko maganar Sheikh Bauchi a wata ganawa da yayi da wakilin jaridar Punch a Najeriya.

A lokacin da Sheikh Dahiru Bauchi yake bada takaitaccen tarihinshi, ya bayyana cewa; “Nayi Auren fari a shekarar 1948.”

Inda ya kara da cewa; “A yanzu haka da nake magana da kai, Allah Ya Yi min baiwa samun ‘Ya’ya 70 da jikoki masu tarin yawa wadanda a yanzu haka duk sun haddace Al-qurani.”

Da yake amsa tambayar ‘Ko wana irin aiki ‘yayan nashi sukeyi?, Sheikh Dahiru Bauchi ya bayyana cewa;

Masu Alaƙa  Gwara dan Ak*yar da zai ga mutane ya kauce hanya ya basu wuri - Sheikh Abdullah Gadon Kaya

“Aikin farko ga ‘yayana shine karatun Al-Qur’ani, daga wannan sai su fara Noma.”

Inda ya bayyana cewa a yanzu haka daga cikin ‘ya’yan nashi akwai Likita, Malaman Addinin Musulunci da kuma Malaman da suke koyarwa a wasu daga cikin Jami’o’in Najeriya.

DABO FM ta binciko daga wata majiya mara tabbaci cewa; Akalla ‘ya’yan Sheikh Dahiru Bauchi guda 26 ne suka kammala karatunsu na Digirin digir-gir yayin da 44 daga ciki kuma suka kammala Digiri na 2 a karatun Boko.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.