Jarumar Indiya ta ki kula Ali Nuhu bayan ya tayata murnar cika shekaru 31

A cikin lamari irin na gaba da gabanta, Fitaccen jarumin fina-finai a Najeriya, Ali Nuhu, ya sha kunya bayan da jarumar Fim ta kasar Indiya ta share shi bayan ya mata magana.

DABO FM ta binciko cewa jaruma, Shraddha Arya, ta kula Ali Nuhu ne bayan ya aike mata da sakon taya murnar ranar zagayowar haihuwarta.

Shraddha Arya, da ta cika shekaru 31, tana yin bikin ranar zagayowar haihuwarta a duk 17 ga watan Agustar kowacce shekara

Ali Nuhu dai ya wallafa sakon ne a ranar Asabar, 17 ga watan Agustar 2019 a kan shafinshi na Instagram.

Sai dai har zuwa yanzu da muke hada wannan rahotan, jarumar bata so “Like” hoton na Ali Nuhu ba, ba ta kuma yi masa martani ko yaya ba.

Masu Alaƙa  Ta tabbata: Jarumar Indiya ta watsa wa Ali Nuhu kasa a Ido bisa kin kulashi da tayi

DABO FM ta gane cewa zuwa yanzu dai Shraddha Arya ta wallafa sakonnin mutane 61 da suka tayata murna a shafin “Story” dake Instagram.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.